Jummaʼa 22 Mayu 2026 - 14:13
Shahid Ra'isi Bai San Dare ko Rana ba Wajen yi wa Jama’a Hidima / Bai Taɓa Tunanin Miƙa Wuya ga Maƙiya ba

Hauza/ Ayatullah al‑Uzma Nuri Hamedani ya bayyana cewa: "Shahid Raisi bai san dare ko rana ba wajen yi wa jama’a hidima, kuma alamun imaninsa ga Allah Madaukakin Sarki sun bayyana sosai a rayuwarsa, ta yadda bai taba mika wuya ga maƙiya ba, amma a gaban jama’a yana da tawali’u da kaskantar da kai."

A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, cikakken sakon Ayatullah Nuri Hamedani dangane da bikin tunawa da cikar shekara biyu da shahadar Ayatullah Sayyid Ibrahim Ra'isi a birnin Qum kamar haka yake:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai.

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu kuma Annabinmu Abul‑Qasim Mustafa Muhammad, da iyalansa tsarkaka, musamman Hujjar Allah a doron kasa, da kuma la’anar Allah ga maƙiyansu har zuwa ranar sakamako.

Ina mika gaisuwa da fatan alheri ga wannan taro mai girma da aka shirya domin tunawa da daya daga cikin fitattun mutane masu hidima ga tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Hujjatul Islam wal Muslimin Sayyid Ibrahim Ra'isi (R).

A cikin tsarin Musulunci, an bayyana wasu ma’auni da ake auna darajar mutane da su, kuma mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne imani da Allah Madaukakin Sarki da kuma ikhlasi a aiki. Wannan abu yana bayyana a cikin dabi’u da halayen muminai. A rayuwar zamantakewa kuma, mafi girman ibada ita ce wacce take jawo yardar Allah.

Saboda haka, daya daga cikin manyan hanyoyin kusantar Allah shi ne yi wa jama’a hidima; wato mutum ya rayu ta yadda kasancewarsa zai zama alheri da anfani ga bayin Allah.

Manzon Allah (SAWA) ya ce: “Abu biyu ne da babu wani alheri da ya fi su: imani da Allah da kuma anfani ga bayin Allah.” A wani hadisin kuma an tambaye shi: wanene mafi soyuwa ga Allah? Sai ya ce: “Mafi alherin mutane shi ne wanda ya fi anfani ga mutane.”

Shahid Ra'isi yana daga cikin mutanen da suka yi kokari a rayuwarsu domin neman yardar Allah, kuma ya sanya ikhlasi a aikinsa a matsayin ginshiki, inda ya sadaukar da dukkan rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima.

A cikin hanyoyin wahala na hidima bai taba gajiya ba, kuma kullum yana la’akari da maslahar Musulunci da juyin juya halin Musulunci. A hidima ga jama’a bai san dare ko rana ba. Alamun imaninsa ga Allah sun bayyana sosai a rayuwarsa, ta yadda bai taba mika wuya ga makiya ba, amma a gaban jama’a yana da tawali’u da kaskantar da kai.

A bangaren biyayya ga jagoranci, riko da jinin shahidai, da kuma manufofin Imam Khumaini da biyayya ga Jagoran Jamhuriyar Musulunci, bai taba nuna shakka ba, kuma har zuwa karshen rayuwarsa yana gabatar da kansa a matsayin sassauƙan dalibi.

Mukamai da matsayi na duniya ba su taba canza ruhinsa ba, kuma wannan ikhlasi da tsoron Allah sun kasance a bayyane a dukkan matakan rayuwarsa. A fannin shari’a, a hidimarsa a Haramin Imam Ridha (AS), da kuma a matsayin shugaban kasa, ya yi amfani da dukkan karfinsa wajen bunkasa kasar.

Ni kaina, bisa sanin da na yi masa na sama da shekaru arba’in, ina bada shaida cewa ya yi iyakar kokarinsa wajen hidima, kuma a karshe ya samu daukakar shahada yayin da yake hidima ga jama’a da kuma cika aikinsa.

Girmama wannan mutum nagari abu ne mai kyau da kuma dacewa, kuma ya kamata a bayyana wa mutane ayyukansa masu amfani da daraja.

A karshe, ina gode wa wadanda suka shirya wannan taro, ina kuma rokon Allah Madaukakin Sarki ya ba kowa nasara.

28 Ordibehesht 1405 (18 ga Mayu, 2026)

Husain Nuri Hamedani

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha